Da yake karin haske game da batun zaman dirshan da masu zanga zanga suke ci gaba da gudanarwa a birnin Khartoum, fadar mulkin kasar, mataimakin shugaban majalissar ta sojoji Mohamed Hamdan Daqlu, ya ce sojoji ba za su tarwatsa masu zanga zangar ba.
A ranar Litinin ne dai TMC da jagororin kungiyoyin 'yan adawa a kasar, suka kammala zaman tattaunawa na uku ba tare da cimma wata yarjejeniya, ta yadda za a kafa gwamnatin farar hula ba.
Bayan tattaunawar ranar Litinin, gungun hadakar 'yan adawar kasar sun yi kira ga 'yan kasar, da su ci gaba da zaman dirshan, tare da gudanar da zanga zangar dare a birnin Khartoum. (Saminu Hassan)