in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta bukaci a lalubo damammakin dake tattare da amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace
2019-04-30 10:49:18 cri

Shugaban sashen takaita yaduwar makamai na ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin, Fu Cong, ya bukaci al'ummomin duniya su lalubo dimbin damammakin dake tattare da amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace.

Fu Cong ya bayyana haka ne yayin zama na 3, na kwamitin share fagen taron bita na bangarorin da suka rattaba hannu kan yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya ta NPT, wanda za a yi a 2020.

Wakilin na kasar Sin ya ce, amfani da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace cikakken 'yanci ne da yarjejeniyar ta NPT ke karfafawa, wanda kuma ke zaman muhimmiyar hanyar da kasashen duniya za su hadu su tunkari kalubalen sauyin yanayi tare, da kara ingiza raya tattalin arzikin duniya, da cimma kare muhalli da muradun ci gaba masu dorewa da ake son cimmawa ya zuwa 2030.

Fu Cong ya kuma yi kira ga dukkan bangarori da su daidaita alakar dake tsakanin hana yaduwar makaman nukiliya da amfanin da makamashin nukiliya ta hanyar da ta dace, karkashin tsarin yarjejeniyar, da inganta hadin kai a kan makamashin nukiliya da kuma daukar managartan matakan samar da karin albarkatu ga kasashe masu tasowa. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China