in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta fitar da sabon jadawalin sassan zuba jarin waje da aka kayyade
2019-04-30 10:29:10 cri

Mahukuntan kasar Sin za su fitar da sabon jadawalin fannonin zuba jari da aka yiwa 'yan kasuwar waje shingen shiga a dama da su. Rahotanni na cewa, za a fitar da sabon jadawalin ne cikin farkon rabin shekarar bana, a wani mataki na kara fadada sassa da 'yan kasuwa baki masu sha'awar zuba jari a Sin za su iya shiga kasuwannin kasar.

Mataimakin ministan kasuwancin kasar Sin Wang Shouwen ya bayyana hakan yayin wani taron manema labarai da ya gudana a jiya Litinin.

Ya ce, yayin da ake sa ran fara aiwatar da dokokin zuba jarin 'yan kasuwar waje da majalissar dokokin kasar Sin ta amincewa tun daga ranar 1 ga watan Janairun shekarar 2020, ma'aikatar cinikayyar kasar na ci gaba da kirkiro dabarun tabbatar da nasarar kudurorin da aka sanya gaba, ta yadda hakan zai samar da kyakkyawan yanayi ga masu ruwa da tsaki.

Jami'in ya ce, ma'aikatar za ta yi duk mai yiwuwa, wajen kare hakkin masu zuba jari na kasashen waje, da samar da kariyar fasaha da suke bukata. Mr. Wang ya kara da cewa, ma'aikatar na shirin fitar da wani kundi na bayanai, wanda zai taimakawa baki masu sha'awar zuba jari a Sin musamman a fannin gudanar da manyan ayyuka.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China