Shugaban kungiyar samar da lambunan shakatawa ta duniya Bernard Ostrom ya bayyana cewa, game da samun ci gaba ba tare da gurbata muhalli ba, Sin ta zama misali a fannoni da dama. Ya yi imani cewa, bikin EXPO na Beijing zai sa kaimi ga kasa da kasa su duba yadda Sin ta kyautata muhalli da kawo zaman rayuwa mai kyau ga jama'a.
Masani kula da batun Sin da Afirka na kasar Kenya Edhurley Cavens ya bayyana cewa, jawabin shugaba Xi Jinping ya shaida imanin Sin na maida hankali ga kiyaye muhalli. A halin yanzu, kasa da kasa suna ganin cewa, Sin tana kokarin shigar da tunanin kiyaye muhalli mai dorewa a cikin aikin raya shawarar "ziri daya da hanya daya", hakan za sa kaimi ga shawarar ta kara samun karbuwa a fadin duniya. (Zainab)