in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Sri Lanka ya haramta rufe fuska bayan hare-haren ranar Easter
2019-04-29 20:36:37 cri
Shugaba Maithripala Sirisena na kasar Sri Lanka, ya haramta sanya duk wata sutura da za ta rufe fuska da ma hana gane fuskar mutum, a matsayin wani matakin tsaro na gaggawa da kasar ta dauka, bayan hare-haren bama-baman ta'addanci da aka kai sassan kasar a lokacin bikin Easter.

Wata sanarwa da ofishin shugaban kasar ya fitar, ta bayyana cewa, dokar hana rufe fuskar za ta fara aiki ne tun daga yau Litinin, karkashin sabbin matakan da suka kai ga sanya dokar ta baci a kasar, domin mayar da martani ga hare-haren bama-baman da suka kai ga kisan sama da mutane 250 tare da jikkata sama da mutane 500. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China