in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin na tsayawa kan hana yaduwar makaman nukiliya ta hanyar siyasa da diflomasiya
2019-04-29 20:14:24 cri

Yau Litinin Geng Shuang, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ya ce, kasar Sin na nacewa kan raya kanta cikin ruwan sanyi, tana kuma himmantuwa wajen raya al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil'Adama. Ta kuma aiwatar da manyan tsare-tsaren nukiliya ne domin kare kanta. Kasar Sin ta kuma yi alkawarin cewa, ba za ta zama kasar da za ta fara amfani da makaman nukiliya ba.

Har ila yau kasar Sin na tsayawa kan hana yaduwar makaman nukiliya ta hanyar siyasa da diflomasiya, ta kuma shiga hadin gwiwar kasa da kasa ta fuskar amfani da makamashin nukiliya cikin lumana da tabbatar da tsaron nukiliya. Kasar Sin za ta ci gaba da kokari wajen inganta yarjejeniyar hana yaduwar makaman nukiliya wato NPT da kara azama kan samun zaman lafiya da tsaro a duniya.

A wannan mako ne, za a gudanar da taro na karshe gabanin babban taron nazarin yarjejeniyar NPT na shekarar 2020 a babban zauren MDD dake New York. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China