in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wani mahari ya hallaka mutum guda tare da jikkata wasu 7 a Baltimoren Amurka
2019-04-29 13:33:39 cri

A kalla mutum guda ne ya rasu, kana wasu 7 suka jikkata, bayan da wani mahari ya bude wuta a garin Baltimore dake jihar Maryland ta Amurka da yammacin jiya Lahadi.

Da yake tabbatar da aukuwar harin, kwamishinan 'yan sandan Baltimore Michael Harrison, ya ce maharin ya tunkari wasu wurare ne guda biyu da ake girka abinci a wani fili, inda nan take ya budewa mutanen da suka taru a wurin wuta da bindiga.

Mr. Harrison ya ce, duk da cewa akwai majami'u guda biyu dake daura da wurin da harin ya auku, amma babu wata alaka tsakanin harin da majami'un.

Jami'in tsaron ya ce, an tsinci gawar wani mutum guda da ya yi yunkurin tserewa harin a kusa da majami'ar dake dandalin Perkins, kana an kai karin wasu mutane 6 asibiti domin ba su jiyya. Ya kara da cewa, akwai kuma wani mutum guda da ya kai kan sa asibiti sakamakon harsashin bindiga da ya same shi a kafa.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China