in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta aiwatar da karin matakan kyautata rayuwar sojojin da suka yi ritaya
2019-04-29 10:27:59 cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin aiwatar da karin matakan kyautata rayuwar sojojin da suka yi ritaya daga aiki. Domin cimma nasarar hakan, an fitar da wasu ka'idoji na saukaka wahalhalun rayuwa da sojojin da suka yi ritaya ke gamuwa da su a fannin inshorar zaman rayuwa.

Babban ofishin kwamitin kolin JKS, da hukumar gudanarwar kasar ne suka fitar da ka'idojin, musamman domin tsofaffin sojojin da ba sa cikin tsarin inshorar zaman rayuwa, ko wadanda suka daina biyan kudi cikin asusun inshorar su saboda karancin kudi, ko rashin aikin yi da suke fama da shi.

Karkashin ka'idojin, an tanaji baiwa irin wadannan tsaffin sojoji damar ci gaba da biyan kudi cikin asusun su na inshora, kana hukumomin dake lura da tsugunar da su su rika biyan wani bangare na ragowar kudin da ya dace tsaffin jami'an su biya.

Ma'aikatar dake lura da al'amuran tsaffin sojojin kasar Sin ta ce, ka'idojin na da nufin samarwa wannan rukuni na al'umma damar cin gajiyar asusun inshore daidai da abun da suka ajiye, za su kuma kare muradun su yadda ya kamata.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China