in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta kara bunkasa kiwon lafiyar tsofaffi
2019-04-29 10:08:10 cri

Mahukuntan kasar Sin sun sha alwashin daukar karin matakan bunkasa kiwon lafiyar tsofaffi. A cewar shugaban hukumar kula da lafiyar kasar Ma Xiaowei, hakan zai kunshi ilmantarwa, da matakan kariya daga kamuwa da cututtuka, da hanyoyin inganta motsa jiki, da samar da jinya da sauran hidimomi ga tsofaffi dake birane da karkara.

Ma ya bayyana hakan ne a jiya Lahadi, yayin wani taron karawa juna sani game da kula da tsofaffi, yana mai cewa, ya zama wajibi a tantance bangaren al'umma da za su ci gajiya daga wannan hidima, a kuma tanaji dukkanin abubuwa da za su bukata yadda ya kamata. Jami'in ya kara da cewa, akwai bukatar yin duba na tsanaki game da sha'anin kudi da za a bukata domin wannan aiki.

Ma ya ce, zuwa karshen shekarar 2018, kasar Sin na da tsaffi 'yan shekaru 60 zuwa sama da suka kai miliyan 249, ana kuma hasashen cewa, wannan adadi zai haura miliyan 300 nan da shekara ta 2025.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China