in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi da shugabannin kasashen waje sun yi rangadin inda ake baje kolin lambunan shakatawa na duniya
2019-04-29 09:36:41 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping da uwargidansa Peng Liyuan, tare da shugabannin kasashen waje da matansu, sun zagaya filin baje kolin lambunan shakatawa na duniya dake yankin arewacin yankin Yanqing na Beijing.

Shugaba Xi Jinping ne ya karbi bakin da suka zo kasar Sin domin halartar bikin baje kolin lambunan shakatawa na duniya na shekarar 2019 na Beijing, a rumfar kasar Sin dake wajen, inda ya gabatar musu da nau'ika daban daban na abubuwan da aka baje da suka hada da furanni da fasahohin lambuna na musammam, wadanda yankuna daban daban na kasar Sin suka gabatar.

A cewar shugaban, ba tsarin kayatattun lambuna kadai rumfar kasar Sin ta gabatar ba, har ma da nuna shirin kasar na raya tsirrai da yayata alfanun ci gaban da za ta samu da sauaran kasashen duniya.

Shugabannin sun kuma ziyarci lambunan kasashen Cambodiya da Jamhuriyar Czech da Djibouti da Kyrgyzstan da Myanmar da Nepal da Pakistan da Japan da Singapore da Tajikistan dake wajen bikin, tare da halartar bikin shuka bishiya. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China