in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AMISOM ta musanta cewa Al-Shabab ta karbe iko da Sabbid
2019-04-29 09:26:26 cri

 

Tawagar kungiyar AU mai aikin wanzar da zaman lafiya a Somalia ko AMISOM a takaice, ta yi watsi da rade radin da ake yadawa cewa wai kungiyar 'yan ta'adda ta Al-Shabab ta sake kwace iko da garin Sabiid wanda aka kwato ba da jimawa ba.

Tawagar ta ce, har yanzu garin wanda ke da nisan kilomita kusan 40 daga kudancin birnin Mogadishu na karkashin ikon dakarun kawancen gwamnatin kasar.

Wata sanarwa da tawagar ta fitar ta ce, dakarun hadakar na ci gaba da aikin wanzar da zaman lafiya a dukkanin sassan kasar, ta kuma bukaci da a yi watsi da duk wani rahoto da ya sabawa hakan.

Sanarwar ta kara da cewa, kungiyar Al-Shabab da masu goya mata baya na jin radadin rasa garin Sabiid, sun kuma damu ganin yadda dakarun kawancen gwamnati ke rike da birnin, don haka a yanzu suka mayar da hankali kan yada farfaganda da zantuka matasa kan gado.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China