Sanawar da ofishin shugaban kasar ya fitar jiya Asabar, ta ce karkashin dokar ta baci, shugaba Sirisena ya dauki matakan ayyana kungiyoyin NTJ da JMI a matsayin haramtattun kungiyoyi a kasar.
A don haka, gwamnati za ta kwace dukkan wasu ayyuka da kadarorinsu. Sanarwar ta kara da cewa, ana daukar matakan haramta sauran kungiyoyin masu tsattsauran ra'ayi karkashin dokar ta baci.
A ranar Talata ne Shugaban kasar ya ayyana dokar ta baci na wucin gadi a kasar, domin kama wadanda ake zargin 'yan ta'adda ne da suka kitsa hare-haren da aka kai majami'u da manyan otel otel a makon da ya gabata. (Fa'iza Mustapha)