A yayin da yake ganawa da shugabannin wasu jam'iyyun Palasdinu a zirin Gaza, Ismail Haniya ya ce, a shirye yake ya gana da jam'iyyu daban daban, musamman ma kungiyar Fatah, don farfado da hadin kai a tsakaninsu.
Tun bayan da Donald Trump ya rike karagar mulkin Amurka, ya fara tunanin yarjejeniyar karni, don wanzar da zaman lafiya a tsakanin Palasdinu da Isra'ila. Sai dai a kwanakin baya, wakilinsa na musamman kan shawarwari, Jason Greenblatt ya fayyace cewa, yarjejeniyar ba za ta kunshi abin da ya shafi kafa kasashe biyu bisa shatin iyakar shekarar 1967 ba. Sau da dama, Palasdinu ta ce ba za ta amince da yarjejeniyar ba, sabo da ba ta shafi batun Kudus da matsalar 'yan gudun hijirarta da kuma matsugunan Yahudawa ba. (Lubabatu)