in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Afirka ta kudu ta yi bikin murnar ranar samun 'yancin kanta
2019-04-28 16:35:51 cri

Kasar Afirka ta kudu, ta yi bikin murnar cika shekaru 25 da samun 'yancin kai da kawar da manufar kariyar ciniki da gudanar da zabe na farko da da ba a bambanta kabilu ba, a jiya Asabar

Shugaban kasar Cyril Ramaphosa da ya halarci bikin ya bayyana a jawabin da ya gabatar cewa, shekaru 25 da suka wuce, al'ummar kasar Afirka ta kudu suka kafa wata sabuwar kasar da ke da zaman daidaito da hadin kan al'umma, inda kuma ba a nuna bambanci ga kabilu da jinsi daban daban, yana mai cewa, rana ce ta walwala ga dukkan al'ummar kasar. Shugaban ya kuma yi alkawarin tabbatar da 'yancin al'ummar kasarsa na jin dadin bunkasar tattalin arziki da zaman rayuwarsu. (Lubabatu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China