in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Botswana ta hada hannu da bankin duniya a bangaren samar da makamashi mai tsafta
2019-04-28 15:47:12 cri
Shugaban Kasar Botswana Mokweetsi Masisi, ya ce kasarsa ta hada hannu da Bankin Duniya, wajen samar da wata dabara kan makamashi mai tsafta da za ta ba kasar karin damar cin gashin kanta a fannin samar da abubuwan da suka shafi makamashi mai tsafta.

Shugaba Masisi, ya bayyana haka ne a wani taron Jam'iyya mai mulkin kasar ta Botswana Democratic Party, wanda ya gudana jiya a birnin Gaborone.

Shugaban ya ce, manufar hadin gwiwar ita ce, lalubo damarmakin da kasar ke da su daga makamashin hasken rana, tare da samar da sabbin sauye-sauyen da za su habaka tattalin arziki da samar da ayyukan yi da ake bukata.

Ya ce tsawon shekaru, Botswana ta kasance tana dogaro kan wutar lantarki daga kasashe makwabta da suka hada da Afrika ta kudu da Mozambique da Namibia.

Sai dai, kasar ta fara fitar da lantarki a bara zuwa turakun lantarki na kungiyar kawancen kamfanonin samar da lantarki na kasashen yankin kudancin Afrika, lamarin da ya sha bambam da lokacin da kasar da ta fi kowacce hakar lu'ulu'u a nahiyar Afrika, ke samun kaso 75 na wutar lantarkin da take bukata daga wasu kasashe. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China