in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka za ta janye daga yarjejeniyar cinikayyar makamai ta duniya
2019-04-27 15:37:07 cri

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa, kasar za ta janye daga yarjejeniyar cinikayyar makamai ta duniya, wadda gwamnatin Obama ta sanyawa hannu.

Donald Trump ya sanar da haka ne a jiya, lokacin da yake halartar taron shekara-shekara na kungiyar kare hakkin mallakar bindiga ta National Rifle Association a birnin Indianapolis na kasar, yana mai cewa, zai janye sa hannun Amurka kan yarjejeniyar dake samun goyon bayan MDD.

Ya kuma bayyana cewa, nan ba da dadewa ba, MDD za ta karbi sanarwar janyewar Amurka a hukumanci.

A shekarar 2013 ne MDD ta amince da yarjejeniyar, wadda ke kayyade cinikayyar makamai a duniya, tun daga kananan makamai har zuwa jiragen yaki na soji. Shugaban kasar na wancan lokaci, Barrack Obama ne ya sanyawa yarjejeniyar hannu, sai dai majalisar dattawan kasar ba ta kai ga amincewa da ita ba.

Fadar White House ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, shugaba Trump zai nemi majalisar dattawan ta ki amincewa da ita.

Ta kuma yi ikirarin cewa, yarjejeniyar ba ta da alkibla, kuma tana yi wa Amurka tarnaki wajen sayar da makamai ga kawaye da abokan huldarta. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China