in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Afirka ta kudu ta yi bikin ranar yaki da cutar zazzabin Maleriya na duniya
2019-04-26 09:55:39 cri

A jiya ne kasar Afirkla ta kudu, ta yi bikin ranar yaki da cutar zazzabin cizon sauro na duniya, tare da alkawarin ganin bayan cutar nan da shekarar 2023.

Sashen kula da harkokin kiwon lafiya na kasar ya bayyana cewa, daga shekarar 2000-2018, an samu raguwar kaso 73 cikin 100 na masu kamuwa da cutar, matakin dake nuna cewa, kasar ta kama hanyar cimma nasarar kawar da cutar a fadin kasar nan da shekarar ta 2023.

Haka kuma, yawan wadanda ke mutuwa a kasar sanadiyar cutar, shi ma ya ragu da kaso 74 cikin 100 a tsakanin wadannan shekaru.

Sai dai kuma, cibiyar nazarin cututtuka masu yaduwa ta kasar(NICD) ta ce, burin kasar na ganin bayan cutar ta Maleriya nan da shekarar 2023, na iya fuskantar kalubale, duba da yadda cutar ke yaduwa da yadda nau'o'in kwayoyin halittar saurayen dake yada cutar ke canjawa.

Duk da haka, hukumar ta NICD, ta ce yadda take ci gaba da sanya ido da gudanar da bincike, ta kara fahimtar kudurin gwamnati na cimma wannan buri.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China