Gwamnatin Tunisia da shirin raya kasashe na MDD da hukumar kula da mata ta MDD ne suka shirya taron, wanda zai gudana har zuwa gobe Juma'a.
A jawabinta na bude taron, Ministar kula da harkokin mata da iyali da yara ta Tunisia, Neziha Labidi, ta ce taron da ake a Tunisia kan daidaiton jinsu, ya nuna yadda kasashen duniya ke sane da kokarin kasar na inganta daidaiton jinsi da hakkokin mata.
Ta kara da cewa, taron dama ce ta bayyana kyakkyawan matsayin Tunisia, inda maza da mata ke aiki tare domin ci gaban kasar, kana kuma take tabbatar da daidaton damarmaki tsakaninsu.
Ta ce dole ne a dakatar da take hakkin mata, ta na mai cewa dole ne dukkan matan kasar, su hada kansu karfafa bada gudunmuwa wajen yanke shawarwari da kuma kasancewarsu kan mukamai. (Fa'iza Mustapha)