in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rwanda na ganin bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing a matsayin dama ta shiga kasuwar kasar Sin
2019-04-25 10:58:58 cri
Hukumar raya kasar Rwanda, ta ce bikin baje kolin lambunan shakatawa na Beijing dake karatowa, zai ba kamfanonin kasar damar kara shiga kasuwar kasar Sin.

Shugaban sashen wayar da kai da tallace-tallace na hukumar, Sunny Ntayombya, ya ce baje kolin dama ce ga kamfanonin kasarsa, ta kara shiga kasuwannin kasar Sin da nufin kara fito da kyayyakinsu zuwa kasuwar.

Ya ce kamfanonin kasar 9 ne za su halarci bikin, wadanda za su gabatar da kayakin marmari da borkono da aka sarrafa da zuma da soyayyen waken kofi da ganyen shayi da kayakin da ake yi su da hannu.

Bikin wanda aka shirya farawa daga ranar 29 ga watan nan, wanda kuma zai shafe kwanaki 162, na da nufin burge bakin da ake sa ran adadinsu ya kai miliyan 16 daga ciki da wajen kasar Sin, da gabatar da tarin tsirrai da furanni da kuma rumfuna masu kayatarwa, tare kuma da dabarun raya muhalli ta hanyar shuke-shuke.

Sama da kasashe da kungiyoyin kasa da kasa 110 da sama da mutane 120 da ba masu gabatar da baje kolin a hukumance ba, sun tabbatar za su halarci bikin, wanda zai zama irinsa mafi samun masu ziyara a tarihi.

Masu baje koli za kuma su gabatar da nasarorin da suka samu a bangaren lambunan shakatawa a dandalin bikin mai fadin muraba'in mita 503 dake kasan babbar ganuwar kasar Sin a lardin Yanqing na Beijing.(Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China