in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta samar da wasu dabarun gano maharan Sri Lanka
2019-04-25 10:31:07 cri

Kasar Morocco ta bayar da wasu dabarun sirri da za su taimaka wajen gano Maharan Sri Lanka.

Sabon shafin watsa labarai ta intanet na kasar Morocco wato Hespress.com, ya ruwaito cewa, hukummomin tattara bayannan sirri na kasar ciki har da hukumar yaki da ta'addanci, sun taka muhimmiyar rawa wajen taimakawa ga cafke 'yan ta'addan da suka kai hari kasar Sri Lanka.

Jerin hare haren bambamai da aka kai kan mujami'u da otel otel a ranar Lahadin da ta gabata lokacin bikin Easter, sun yi sanadin mutuwar mutane a kalla 359 a kasar Sri Lanka.

A cewar rundunar 'yan sandan Sri Lanka, kusan mutane 60 aka kama tun bayan aukuwar iftila'in. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China