Babban jami'in kamfanin Andrew Chimphondah, shi ne ya shaidawa manema labarai hakan a birnin Nairobin kasar Kenya, yayin shirin samun horo na PPP da aka shiryawa masu raya kadarori da 'yan kwangila da kamfanin ya shirya. Yana mai cewa, gwamnati ita kadai ba za ta iya magance karuwar bukatar giudajen kwana a Afirka ba.
Don haka, kamfanin ya karfafawa gwamnatocin nahiyar gwiwa, da su kafa alaka da sassa masu zaman kansu, a matsayin wani muhimmin mataki na samar da gidajen kwana masu yawa kuma cikin farashi mai sauki.
Chimphodah ya ce, karkashin wannan tsari, gwamnatoci za su samar da filaye da kayayyakin more rayuwa, yayin da sassa masu zaman kansu za su samar da kudaden da ake bukata wajen gina rukunan gidajen kwana masu saukin kudi.
A cewarsa, tsadar filaye a galibin yankunan biranen kasashen Afirka, shi ke kawo tsaiko wajen gina gidajen kwana masu saukin kudi.(Ibrahim)