in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta fadada hadin gwiwa da sauran sassa a fannin binciken sararin samaniya
2019-04-24 20:13:35 cri

Mahukunatan kasar Sin sun jaddada aniyar kasar, ta kara fadada ayyukan binciken sararin samaniya, ta hanyar hadin gwiwa da sauran sassan masu ruwa da tsaki, a wani mataki na karfafa gudummawar ta, game da burin cimma muradun MDD na ci gaba mai dorewa.

Da yake gabatar da wannan tsokaci, mataimakin shugaban hukumar kula da aikin binciken sararin samaniya ta Sin Mr. Wu Yanhua, ya ce Sin za ta kafa wani tsari na hadin gwiwa, domin cimma moriya tare da sauran kungiyoyi da cibiyoyin kasa da kasa, masu bincike game da wannan fanni, za kuma ta shiga a dama da ita wajen bunkasa masana'antun samar da kayan binciken samaniya, da tabbatar da dorewar ayyukan.

Wu Yanhua, ya ce bisa burin ta na samar da karin hidimomi ga kasashen da suka rungumi shawarar ziri daya da hanya daya, musamman kasashe masu tasowa, kasar Sin na gina wani tsari na musayar bayanan binciken samaniya, da musayar gajiyar da ake samu daga taurarin bil Adama.

Jami'in ya kara da cewa, Sin za ta tabbatar da inganta cin gajiya daga albarkatun tauraron dan Adam masu nasaba da ayyukan kiwon lafiya, da kandagarki da magance barkewar annoba, da samar da ilimi daga nesa, da baiwa al'umma kariyar tsaro.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China