in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Morocco ta kame wasu mutane shida dake da alaka da IS
2019-04-24 11:09:23 cri
Ma'aikatar harkokin cikin gidan kasar Morocco ta bayar da sanarwa jiya Talata cewa, babbar hukumar binciken dokokin shari'a ta kasar ta kame wasu mutane shida wadanda ke da alaka da kungiyar IS a birnin Sale dake arewacin kasar.

Sanarwar ta ce, mutanen shida, masu shekaru 22 zuwa 28 da haihuwa, sun yi yunkurin kera abubuwan fashewa gami da kaddamar da hare-haren ta'addanci a Morocco. 'Yan sanda sun kuma kwace wasu na'urorin sadarwa da wukake tare kuma da wasu littattafan dake yada tsattsauran ra'ayi a yayin samamen da suka kaddamar.

A watan Mayun shekara ta 2003 ne, aka kai harin ta'addanci a birnin Casablanca dake arewacin Morocco, harin da ya hallaka tare da jikkata mutane da dama. Daga baya ne kuma gwamnatin Morocco ta fara daukar wasu matakan yaki da ta'addanci, inda aka samu nasarori da dama. Alkaluman sun yi nuni da cewa, daga farkon shekarar 2015 zuwa watan Yunin shekara ta 2018, an murkushe kungiyoyin 'yan ta'adda 53 a Morocco, tare da mika mutane 815 da ake zargi ga hukumomin shari'a. (Murtala Zhang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China