in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
UNICEF: An kashe yara 45 a hare-haren ta'addancin kasar Sri Lanka
2019-04-24 10:51:46 cri
Asusun kula da kananan yara na MDD (UNICEF) ya bayyana a jiya Talata da cewa, ya girgiza matuka da hare-haren da aka kaiwa iyalai ciki har da kananan yara a majami'u da ote-otel a lokacin bikin Easter, a kasar Sri Lanka.

A wata sanarwar da kakakin Asusun Christophe Boulierac ya fitar a Geneva na kasar Switzerland, ya ce hare-haren da aka kaddamar a wurare daban daban na kasar Sri Lanka sun haddasa mutuwar yara 45.

A cewarsa, bam da ya tashi a majami'ar St Sebastian's dake Katuwapitiya kadai ya sabbaba mutuwar yara 27 tare da jikkatar wasu 10.

Sa'an nan a garin Batticaloa, yara 13 ne suka rasa rayukansu, kana mafi kankanta a cikinsu shi ne wani jariri dan watanni 18 a duniya. Sauran yara 5 wadanda shekarunsu ke tsakanin 7 zuwa 16 suna samun jinya a asibiti yanzu.

Wasu asibitocin da aka kwantar da irin wadannan yara, na bukatar muhimman kayayyakin kiwon lafiya, kuma asusun na UNICEF yana kokarin samar da irin wadannan muhimman kayayyakin kiwon lafiya da ake bukata.

Asusun ya ce, yaran da bala'in ya raba da 'yan uwansu, na bukatar taimako don gano tare da sake hada su da iyalansu. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China