in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres: Shawarar "ziri daya da hanya daya" wata muhimmiyar dama ce ga duniya
2019-04-24 09:53:29 cri
Babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa shawarar "ziri daya da hanya daya" da kasar Sin ta gabatar, wata muhimmiyar dama ce ga duniya baki daya.

Guterres wanda ya bayyana hakan yayin zantawa da manema labarai na kasar Sin a hedkwatar MDD, kafin ya tashi zuwa kasar Sin don halartar babban taro na biyu na dandalin hadin gwiwar kasa da kasa game da shawarar "ziri daya da hanya daya" da zai gudana a birnin Beijing, fadar mulkin kasar ta Sin. Ya ce, shawarar ta samar da alakar zuba jari masu tarin yawa tsakanin kasashen duniya. Hakan wata dama ce da za ta karfafa aiwatar da manufofin samun ci gaba mai dorewa, kana wata muhimmiyar dama ta kaddamar da matakan kare muhalli cikin shekaru masu zuwa.

Jami'in na MDD ya ce, shawarar wata muhimmiyar dama ce ta taimakawa kasashe masu tasowa, ta yadda za su cimma nasarar manufofin samun ci gaba mai dorewa, da ajandar MDD nan da shekarar 2030, duba da matsalar kudaden da ake fuskanta da ma matsalar canjin yanayin duniya dake karuwa da yadda kasashen duniya suka gaza cimma alkawuran da suka yi a taron Paris.

Don haka, ya ce, bunkasa zuba jari tsakanin kasa da kasa, abu ne mai matukar muhimmanci, musamman wajen aiwatar da ajandar da MDD ke fatan cimmawa nan da shekarar 2030. (Ibrahim Yaya)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China