in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Tattalin arzikin masana'antun Sin yana gudana lami lafiya a rubu'in farko na bana
2019-04-23 19:28:09 cri

Kakakin watsa labarai na ma'aikatar kula da masana'antu da sadarwa ta kasar Sin Huang Libin, ya bayyana a nan birnin Beijing yau Litinin cewa, tattalin arzikin masana'antun kasar Sin yana gudana lami lafiya a cikin rubu'i na farkon shekarar bana, kuma matsin lambar da kasar take fuskantar a fannin ya ragu sannu a hankali.

An ce, dalilin da ya sa tattalin arzikin masana'antun kasar ke gudana cikin lumana shi ne, gwamnatin kasar tana aiwatar da manufufin da suka dace, misali rage harajin da kamfanoni matsakaita da kanana suke biya, da soke wasu kudaden da suke biyan hukumomin gwamnati, da sauransu.

Kakakin ya kara da cewa, nan gaba kasar Sin za ta ci gaba da bude kofa ga kasashen ketare a bangaren masana'antu. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China