Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Geng Shuang, ya bayyana a yayin taron ganawa da manema labaran da aka saba yi a nan birnin Beijing a yau din nan cewa, kasar Sin ta yi suka da kakkausar murya, game da jerin hare-haren da aka kaddamar a kasar Sri Lanka, haka kuma tana son yin kokari tare da sauran kasashen duniya, domin kara karfafa hadin gwiwar dake tsakaninsu a bangaren yaki da ta'addanci, tare kuma da kiyaye zaman lafiya da kwanciyar hankali a shiyya shiyya, da kuma duk fadin duniya.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, bayan hare-hare sau takwas da aka kai a kasar ta Sri Lanka, hukumar 'yan sandan kasar ta gano, ta kuma rushe na'urar boma-bomai ta tara da aka girke cikin nasara.
Geng Shuang ya kara da cewa, gwamnatin kasar Sin za ta ci gaba da dora muhimmanci kan wannan lamarin. (Jamila)