in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Mali ya nada sabon firaministan kasar
2019-04-23 10:27:32 cri
Gidan talibijin na kasar Mali ya sanar da umurnin da shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keïta ya rattaba hannu a kai, inda aka nada Boubou Cisse a matsayin sabon firaministan kasar.

Boubou CISSE yana da digiri na uku a fannin tattalin arziki, ya kuma taba aiki a bankin duniya, a shekarar 2013 ya zama ministan masana'antu da ma'adinai a gwamnatin farko bayan Boubacar Keïta ya lashe zaben shugabancin kasar ta Mali, har zuwa shekarar 2016 inda aka nada shi a matsayin ministan tattalin arziki da harkokin kudi na kasar.

Magabacin Cisse, tsohon firaministan kasar Ousmane Issoufi Maiga ya yi murabus ne a ranar 18 ga watan. Sakamakon tashin hankalin da ya faru a 'yan kwanakin da suka wuce, da kuma kalubalen ta'addanci da har yanzu ake fuskanta. Majalisar dokokin kasar ta Mali ta yi shirin jefa kuri'ar yanke kauna ga gwamnatin Maiga a ranar 19 ga wata. Kafin haka, dakaru masu adawa da gwamnati da shugabannin addinin musulunci da kuma wasu 'yan jam'iyya mai mulkin kasar, sun yi ta yin zargin cewa, gwamnatin Maiga ita ce babban dalilin da ya sanya aka kasa gudanar da harkokin kasar yadda ya kamata. (Bilkisu Xin)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China