in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Rundunar sojojin ruwan kasar ta yi bikin cika shekaru 70 da kafuwa
2019-04-23 10:16:22 cri

A jiya ne sojojin ruwan kasashen duniya suka yi wani atisaye a birnin Qiandao mai tashar jiragen ruwa dake yankin gabashin kasar Sin, don murnar bikin cika shekaru 70 da kafa rundunar sojojin ruwa ta PLA ta Sin.

A jawabinsa yayin bikin, kwamandan rundunar sojojin ruwan kasar Sin Shen Jinlong, ya ce an shirya shagulgulan ne, don karfafa musaya da amincewa da juna da bunkasa hadin gwiwa tsakanin sojojin ruwan kasashe daban-daban.

Shen ya ce, a shirye sojojin ruwan kasar Sin suke, su hada kai da takwarorinsu na sauran kasashe, da kulla abota da hadin gwiwa bisa daidaito tsakaninta da takwarorinta na na ketare, da nufin taimakawa juna da alakar samun nasara tare, da shiga da dama da su cikin ayyukan samar da zaman lafiya da kwanciyar hankali a duniya.

Shagulgulan na kwanaki hudu, za su mayar da hankali ne kan ayyukan da suka hada da fareti, tarukan karawa juna sani, da musayar al'adu da wasanni.

Tawagogin sojojin ruwa daga sama da kasashe 60 ne sun iso kasar Sin kuma za su halarci bikin. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China