in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta daina ba da kariya ga wasu kasashe da yankuna da suka sayi man fetur daga Iran
2019-04-23 10:01:11 cri

A jiya ne, fadar White House ta kasar Amurka ta ce, gwamnatin kasar ta daina ba da kariya ga wasu kasashe da yankuna da suka sayi man fetur daga Iran, wadda Amurka ta sanya wa takunkumi, a kokarin hana Iran din sayar da man fetur din ta.

A cikin sanarwar da aka fitar a jiya, Fadar White House ta ce, a farkon watan Mayun bana ne wa'adin matakin Amurka na ba da irin wannan kariya ga wasu kasashe da yankuna zai cika, kuma Amurka ba za ta ci gaba da ba da kariyar ba. Nufinta shi ne hana Iran sayar da man fetur dinta baki daya, wanda Iran din ke dogaro a matsayin kudin shigarta. Haka kuma Amurka za ta ci gaba da matsa wa Iran lamba ta fuskar tattalin arziki saboda barazanar da take haifarwa.

Sanarwar ta kara da cewa, Amurka za ta hada kai da kasashen Saudiya, hadaddiyar daular Larabawa wato UAE da sauran aminanta daukar matakan tabbatar da ganin an samar da isasshen man fetur a kasuwar duniya.

A watan Nuwamban bara ne, Amurka ta sake sanya wa Iran takunkumi ta fuskar makamashi da hada-hadar kudi. Amma ta ba da kariya ga kasashen Indiya, Turkiya da sauran kasashe ko yankuna 6 kariya ta wucin gadi da su sayi man fetur daga Iran, a kokarin tabbatar da samar da isasshen man fetur a duniya. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China