in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kwamitin sulhu ya yi Allah wadai da jerin hare-haren ta'addanci da aka kai Sri Lanka
2019-04-23 09:42:20 cri

Kwamitin sulhu na MDD ya yi Allah wadai da kakkausar murya kan jerin hare-haren ta'addanci da aka kaddamar a kasar Sri Lanka.

Cikin wata sanarwa da kwamitin ya fitar a jiya, ya bayyana harin na rashin Imani a matsayin mai tayar da hankali. Mambobin kwamitin sun kuma mika ta'aziya da jaje ga iyalan wadanda suka rasa rayuka, gami da gwamnatin kasar Sri Lanka, tare da fatan ganin wadanda suka ji rauni za su samu sauki cikin hanzari.

Kwamitin sulhun ya kara da cewa, dole ne a zakulo wadanda suka kaddamar da hare-haren, da wadanda suka goya musu baya, don gurfanar da su a gaban kotu. Sa'an nan kwamitin ya bukaci gamayyar kasa da kasa da su hada kai da gwamnatin kasar Sri Lanka da sauran hukumomi masu ruwa da tsaki, bisa dokokin kasa da kasa, gami da kudurorin kwamitin sulhun. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China