Majalisar ta bayyana cikin wata sanarwa cewa, ta ba da wasu shawarwari masu muhimmanci da kuma dokoki bisa kundin tsarin mulki dangane da yiwa hukumomin kasar gyaran fuska ciki har da dakatar da wasu jakadu daga aiki.
Bugu da kari, majalisar ta yanke shawara a yayin ganawar da ta yi jiya Litinin, don sake nazartar kudaden ketare da aka kashe da kudaden harajin fitar da kayayyaki dake babban bankin kasar
Aikin majalisar wadda karkashin jagorancin Abdel-Fattah Al-Burhan dai, shi ne tafiyar da harkokin kasar, bayan kifar da gwamnatin shugaba Omar a-Bashir. (Ibrahim Yaya)