Moussa Faki ya bayyana hakan ne yayin da yake kaddamar da sabon shirin nahiyar, wanda ke bukatar zage damtse tsakanin kasashen mambobin kungiyar,da hukumomin kungiyar da ma ragowar masu ruwa da tsaki,idan har ana son shirin ya kai ga gacci.
Kungiyar ta ce, manufar sabon shirin, ita ce, samar da damammaki ga matasa miliyan guda dake sassan nahiyar daban-daban, a muhimman fannoni da suka hada da aikin yi,da sana'o'i, Ilimi da shiga a dama da su a wadannan fannoni hudu(4E's), matakan da za su hanzarta bunkasar rayuwa da tattalin arziki a nahiyar.
A gobe ne dai ake sa ran kaddamar da sabon shirin a hedkwatar kungiyar ta AU dake birnin Addis Ababa na kasar Habasha a hukumance.(Ibrahim)