Mai magana da yawun fadar shugaban kasar Afirka ta kudu Khusela Diko wanda ya bayyana hakan cikin wata sanarwa da aka rabawa manema labarai jiya Litinin, ya ce, shugaba Ramaphosa zai halarci taron gaggawan da za a kira, domin ba da gudummawa ga manufar da AUn ke fatan cimmawa na kawar da karar bindigogi a nahiyar nan da shekarar 2020.
Sanarwar ta ce, shugaba Ramaphosa zai halarci taron kolin Masar, inda zai mayar da hankali kan yanayin siyasa sa tsaro da ake fama da shi a kasashen Libya da Sudan.
Shugaba Abdel-Fattah al-Sisi na kasar Masar, ya kira taron ne a matsayinsa na shugaban karba-karba na kungiyar AU. Shi dai taron AU na Masar din, ya kunshi kasashen Masar kasancewar mai rike da shugabancin karba-karba, da Afirka ta kudu, mai jiran gadon shugabancin karba-karba na kungiyar, sai kuma Rwanda wanda wa'adinta shugabancinta ya kare.
Taron kolin zai kuma samu halartar shugaban hukumar gudanarwar kungiyar Moussa Faki Mahamat, wanda ake sa ran zai gabatar da rahoto game da matakan da kungiyar ta dauka na daidaita rikicin kasashen Sudan da Libya. (Ibrahim Yaya)