in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kaddamar da dandalin kasa da kasa kan kirkire-kirkiren watsa labarai ta fasahohin zamani na 5G da 4K
2019-04-22 19:52:05 cri

A gabannin dandalin koli kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu, yau Litinin an kaddamar da dandalin kasa da kasa kan kirkire-kirkire wajen watsa labarai, ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani na 5G da 4K a nan birnin Beijing, dandalin da ya samu mahalartar wakilai sama da 150 na kafofin watsa labarai fiye da 50, wadanda suka zo daga kasashe da yankina 25 a fadin duniya.

Mataimakin ministan zartaswa na ma'aikatar yada manufa ta kasar Sin Wang Xiaohui ya halarci dandalin kuma ya sanar da cewa, za a fara watsa shirin bidiyo mai taken "mu gina makoma tare", wanda aka shirya shi musamman, domin dandalin koli kan hadin gwiwar dake tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na biyu.

Wakilan da suka halarci dandalin sun yi tattaunawa kan batutuwa, game da yadda za a cimma burin yin kirkire-kirkire kan aikin watsa labarai, da kuma yadda za a kara zurfafa hada kai tsakanin kasa da kasa a bangaren a sabon zamanin da ake ciki. Mataimakin ministan ma'aikatar yada manufa ta kasar Sin, kuma shugaban babban rukunin gidajen telibijin da rediyo na kasar Sin wato CMG Shen Haixiong ya gabatar da wani jawabi yayin dandalin, inda ya bayyana cewa, babban rukuninsa yana himmantu kan aikin tsara sabon salon ci gabansa, ta hanyar yin amfani da sabbin fasahohin zamani na 5G da 4K, da kuma kwaikwayar tunanin bil Adama ko AI, haka kuma yana fatan rukunin CMG zai yi kokari tare da kafofin watsa labaran kasashe, da yankuna wadanda suka shiga shawarar ziri daya da hanya daya, bisa tushen tattauna da juna, da cimma moriyar juna, ta yadda za a ingiza cudanyar al'adun dake tsakanin kasa da kasa.

Yayin dandalin, an kuma fitar da takardar kirkire-kirkiren watsa labarai ta hanyar yin amfani da fasahohin zamani na 5G da 4K, domin gudanar da hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa a bangaren samar da shirye-shiryen telibijin a kasashen dake kan hanyar siliki, inda aka jaddada cewa, nan gaba za su ci gaba da yin kokari tare, domin ciyar da kafofin watsa labaran kasashe daban daban gaba, bisa tushen daidaito da moriyar juna a sabon zamanin da ake ciki, tare kuma da taka sabuwar rawa, ta gina al'umma mai kyakkyawar makoma ga dukkan bil Adama.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China