in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sharhi: Shugaban kasar Sin ya aike da amsa game da wasikar da wasu dalibai Amurkawa suka rubuto masa
2019-04-22 19:43:41 cri

A 'yan kwanakin nan, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da amsa game da wasikar da wasu dalibai Amurkawa suka rubuto masa, domin amsa tambayoyin da suka yi masa, baya ga karfafa zukatansu wajen bayar da gudummawa ga kyautatar dankon zumunci a tsakanin jama'ar Sin da Amurka. Wadannan dalibai fiye da 40 dai na daga ajin koyon harshen Sinanci na makarantar North Niles da ke jihar Illinois, ta kasar Amurka.

Wannan dai wasika ce da ya rubuta da kansa, domin inganta cudanyar al'ummar kasashen biyu. Sinawa kan ce, tushen raya hulda a tsakanin kasa da kasa shi ne cudanya da fahimtar jama'arsu. Kara fahimtar al'umma zai sa kaimi ga gwamnati wajen daukar matakan sada zumunta, da kuma kiyaye ci gaban huldar kasashen yadda ya kamata.

Sakamakon halin sauyawa da duniya ke ciki, Sin da Amurka na samun takaddama da dama. Kuma Sin a matsayinta na kasa mai tasowa, kana Amurka a matsayinsa na masa mai ci gaba mafi girma a duniya, dangantakarsu na samun babban canji.

Sinawa masu son bude ido na kara fahimtar Amurka, amma akwai dimbin Amurkawa dake nuna bambancin ra'ayi ga kasar Sin bisa labarai na rashin gaskiya, wadanda kafofin watsa labarai na Amurka suke bayarwa. Sakamakon haka, ya kamata a kara yin cudanyar al'ummar Sin da Amurka, a maimakon dakatar da cudanyar ta hanyar "rufe kofa" da kuma "korar Sinawa daga Amurka".

A karshen wannan wasikar da shugaba Xi ya rubuta, ya gabatar wa daliban Amurkawa goron gayyata cewa, "Gani ya kore ji, ina maraba da zuwanku kasar Sin". A hakika ma dai, duk wanda ke da niyyar fahimtar kasar Sin, da ba da gudummawarsa ga kara fahimtar juna, da amincewar juna, kasar Sin na maraba da zuwansu.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China