in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyar jerin hare-haren Sri Lanka ya karu zuwa 290
2019-04-22 13:57:58 cri
Rundunar 'yan sandan kasar Sri Lanka ta bayyana cewa, adadin mutanen da suka mutu sanadiyar jerin abubuwan fashewar da suka girgiza kasar, ya karu zuwa 290, yayin da sama da 500 kuma suka jikkata.

Rahotanni farko, sun bayyana cewa, adadin wadanda suka mutu sun kai 228, kana 450 kuma suka jikkata a hare-hare guda takwas din da aka kai ranar Lahadi a majami'u uku da otel-otel guda hudu dake sassan kasar.

Wata sanarwa da hukumar raya harkokin yawon shatakawa ta kasar ta fitar jiya Lahadi, ta bayyana cewa, baki 'yan kasashen waje 32 na daga cikin wadanda suka mutu, sanadiyar wadannan hare-hare.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China