in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Pompeo ya zanta da shugaban Afghanistan ta wayar tarho kan tattaunawar zaman lafiya
2019-04-22 11:23:45 cri
Sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo ya zanta da shugaban Afghanistan Mohammad Ashraf Ghani ta wayar tarho kan tattaunawar zaman lafiya da ta cije tsakanin shugabannin kasar da kungiyar Taliban.

Wata sanarwa da kakakin ma'aikatar harkokin wajen Amurka Morgan Ortagus ya fitar na nuna cewa, Pompeo ya bayyana rashin jin dadin kasarsa game da jinkirta tattaunawar bangarorin biyu, inda ya yi kira da a gaggauta kiran taron a Doha, babban birnin kasar Qatar.

A baya dai, an shirya gudanar da taron ne tsakanin ranakun 19 zuwa 21 ga watan Afrilu a birnin na Doha, don lalulo hanyoyin daidaita tashin hankalin kasar. Amma tattaunawar ta gamu da cikas a ranar Alhamis din da ta gabata, biyo bayan rikicin cikin gida da korafe-korafen da Taliban ta gabatar game da wakilan tawagar gwamnati a tattaunawar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China