in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin kasar Sin sun aikawa takwarorinsu na kasar Sri Lanka sakon ta'aziya dangane da munanan hare-haren da aka kai a sassan kasar
2019-04-22 10:40:19 cri
Shugaba Xi Jinping na kasar Sin da firaministan kasar Li Keqiang, sun aikawa takwarorinsu na kasar Sri Lanka sakon ta'aziya, bi da bi, bayan jerin munanan hare-haren da suka girgiza kasar.

A sakonsa ga takwaransa na Sri Lanka, shugaba Xi ya bayyana cewa, ya kadu matuka da samun labarin jerin abubuwan fashewar da suka tashi a kasar, wadanda suka jikkata mutane da dama.

Shugaba Xi ya ce, a madadinsa da gwamnati da kuma al'ummar Sinawa, yana mika sakon ta'aziya ga 'yan uwa da iyalan wadanda suka rasa rayukansu, tare da jajantawa iyalan wadanda suka jikkata.

Ya ce, gwamnatin kasar Sin da daukacin Sinawa, za su kasance tare da al'ummar Sri Lanka, suna kuma goyon bayan kokarin gwamnatin Sri Lanka na tabbatar da zaman lafiya da tsaro a kasar.

Shi ma firaministan kasar Li Keqiang, ya aikawa takwaransa na Sri Lanka Ranil Wickremesinghe sakon ta'aziya dangane da hare-haren da aka kai a sassan kasar.(Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China