Rundunar 'yan sandan kasar, ta ruwaito rahotannin kafafen watsa labarai na cewa, an mika mutane 10 cikin 13 da aka kama a Colombo, babban birnin kasar ga sashen binciken manyan laifuffuka.
Firaministan kasar Ranil Wickremesinghe ya shaidawa manema labarai cewa, mutanen da aka kama 'yan kasar Sri Lanka ne, ana kuma gudanar da bincike don kara gano wadanda ke da hannu a tashin abubuwan fashewar.
Ya ce, kimanin mutane 228 ne aka tabbatar sun mutu kana wasu 450 kuma sun jikkata, sanadiyar abubuwan fashewa takwas din da suka tashi a jiya Lahadi. (Ibrahim)