in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hare haren da aka kai Sri Lanka ya karu zuwa 138
2019-04-21 16:35:05 cri

Adadin wadanda suka mutu sanadiyyar hare-haren da aka kai kasar Sri Lanka yau Lahadi, ya karu zuwa 138, inda mutane sama da 500 suka jikkata.

A sakonsa na musammam da aka watsa ta kafafen yada labarai, Shugaba Maithripala Sirisena, ya bukaci jama'ar kasar su kwantar da hankalinsu tare da ba hukumomi hadin gwiwa, domin gaggauta gudanar da bincike kan hare-haren.

Ya kuma yi kira ga jama'a su kauracewa yada labaran karya, har sai sun tabbatar da sahihancinsu.

Gwamnatin Sri Lanka ta ce ana gudanar taron gaggawa na majalisar kula da tsaro ta kasar, wanda ya samu halartar firaministan kasar Ranil Wickremesinghe.

Rundunar 'yan sandan kasar wadda ta ce mujami'u 3 da otel 3 aka kai wa hare-haren, ta ce an tsaurara matakan tsaro a kasar.

Har kawo yanzu, babu wanda ya dauki alhakin kai harin. (Fa'iza Mustapha)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China