Kasar Sin ta harba sabon tauraron dan Adam na BeiDou zuwa sararin samaniya daga cibiyar harba tauraron dan Adam na Xichang dake lardin Sichuan da misalin karfe 10:41 na safiyar jiya Asabar.
Linzamin Long March-3B ne ya harba tauraron, wanda shi ne na 44 cikin dangin taurarin BeiDou, kuma irinsa na farko dake juyawa a lokaci guda da duniyar dan Adam.
Bayan gudanar da shawagi na gwaji, tauraron zai yi aiki da wasu taurarin BeiDou 18 a matsakaicin mataki tsakanin sararin samaniya da duniyar bil adama.
Babban wanda ya tsara tauraron Yang Changfeng, ya ce irin wannan tsarin, inda rukunonin taurari 3 ke shawagi a tare, abu ne da ake samu kadai a taurarin BeiDou kuma shi ne irinsa na farko a duniya
Ya ce harba tauraron zai kara yawan taurarin dan Adam da ake iya gani a yankin Asiya da Fasifik tare da inganta yi wa yankin hidima. (Fa'iza Mustapha)