in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Syria da Rasha sun tattauna kan shawarwarin game da batun Syria na sabon zagaye
2019-04-20 16:41:59 cri
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad, ya tattauna a jiya, da Alexander Lavrentyev, manzon musamman na shugaban kasar Rasha kan batun Syria, kan sabon zagayen shawarwari game da batun Syria da za a shirya a Astana, inda bangarorin biyu suka tattauna kan batutuwan da suka shafi sabon zagayen shawarwarin, tare kuma da jaddada muhimmancin cimma matsaya tsakanin kasashen Syria da Rasha kan batutuwan.

Kamfanin dillancin labaru na kasar Syria ya ruwaito cewa, bangarorin biyu sun kuma tattauna kan musayar fursunoni, da tantance inda mutanen da suka bata suke da dai sauran matsaloli.

A yayin tattaunawar, Bashar al-Assad ya bayyana cewa, akwai bukatar a dauki matakai don kawar da cikas, da nufin tabbatar da yarjejeniyoyin da suka shafi lardin Idlib na kasarsa, wadanda ke bada muhimmanci kan kawar da "kungiyoyin 'yan ta'adda" dake shiyyar.

A nasa bangaren, Alexander Lavrentyev, ya bayyana imaninsa kan ci gaban da za a samu a yayin shawarwarin na Astana game da batutuwan yaki da ta'addanci, da yunkurin siyasar Syria, da kafa kwamitin tsarin mulki, da tantance inda mutanen da suka bata cikin yaki suke, da kuma 'yan gudun hijira da dai sauransu.

An ce, za a shirya shawarwarin na Astana a tsakanin ranar 25 zuwa 26 ga wata, inda za a mai da hankali kan tattauna yanayin da Syria ke ciki, musamman ma yanayin yankin Idlib da na arewa maso gabashin kasar, da kafa kwamitin tsarin mulki a kasar, da daukar matakan amincewa juna tsakanin bangarori daban daban na Syria, da inganta komawar 'yan gudun hijira da wadanda suka rasa gidajensu a gida, da kuma kyautata yanayin jin kai da dai sauransu. (Bilkisu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China