in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An yi nunin sakamakon hadin gwiwa tsakanin Sin da Najeriya bisa shawarar ziri daya da hanya daya
2019-04-18 10:48:47 cri

An yi bikin nune-nunen sakamakon da kasar Sin da tarayyar Najeriya suka samu, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da bikin nune-nunen sakamakon cudanyar dake tsakanin kamfanonin kasashen biyu a Abuja, fadar mulkin Najeriya tsakanin ranekun 15 zuwa 17 ga wata, inda kuma aka shirya taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu, domin share fagen dandalin tattaunawar koli kan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2, wanda za a gudana a birnin Beijing ba da dadewa ba.

Babbar kungiyar 'yan kasuwan kasar Sin dake tarayyar Najeriya ce ta shirya wannan bikin nune-nune, na sakamakon da kasashen biyu suka samu yayin da suke gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya, da bikin nune-nune sakamakon cudanyar dake tsakanin kamfanonin kasashen biyu, a bakin shigar cibiyar taron kasa da kasa na Abuja, an ga wani bango mai fadin mitoci 18, inda aka buga hotuna iri daban daban kan sakamakon da kasashen biyu suka samu, yayin da suke gudanar da hadin gwiwa dake tsakaninsu bisa shawarar ziri daya da hanya daya.

Babban sakataren babbar kungiyar 'yan kasuwan kasar Sin dake tarayyar Najeriya Cui Guangzhen ya bayyana cewa, an shirya wannan bikin nune-nunen ne a gabannin dandalin tattaunawar koli kan hadin gwiwa tsakanin kasa da kasa bisa shawarar ziri daya da hanya daya karo na 2 da za a gudanar a birnin Beijing, makasudin shirya bikin shi ne yada manufa ga bangarori daban daban na Najeriya game da shawarar ziri daya da hanya daya, da kuma sakamakon da aka samu a Najeriya tun bayan da aka kira taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasashen Afirka, yana mai cewa, "Mun yi cikakken bayani kan sakamakon da aka samu tun bayan da aka fara aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, kana mun yi nune-nune kan sakamakon da aka samu a Najeriya, tun bayan da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da shirin game da ayyuka guda takwas, yayin taron kolin Beijing na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da Afirka; Misali ingiza ci gaban masana'antu, da gina kayayyakin more rayuwar jama'a, da kara kwarewar aikin hukumomin gwamnati, da kyautata cinikayya, da samar da taimako ga Najeriya da sauransu."

Najeriya kasa mafi saurin ci gaban tattalin arziki ne a Afirka, hadin gwiwar tattakin arziki da cinikayya dake tsakanin kasar Sin da Najeriya zai sa sassan biyu su ci gajiya matuka, ko shakka babu yana da babban boyayyen karfi, da makoma mai haske, a don haka domin sa kaimi kan cudanyar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin sassan biyu, babbar kungiyar 'yan kasuwar kasar Sin dake Najeriya ta shirya bikin nune-nune kan sakamakon da kamfanonin kasashen biyu suka samu, yayin da suke gudanar da hadin gwiwar dake tsakaninsu sau biyu a kowace shekara, Cui Guangzhen ya ce, "Adadin kamfanonin da suka shiga bikin nune-nunen ya kai sama da 50, wuraren nune-nunen da aka kebe sun kai wajen 100, kamfanonin sun hada da na gina kayayyakin more rayuwa, da na cinikayya, da na samar da kayayyakin gini, da na kere-kere, da kuma masu samar da hidimar harkar kudi da sauransu."

Yayin bikin, ban da wasu manyan kamfanoni karkashin mallakar gwamnatin kasar Sin kamar su CCECC, da CHEC, da CRCC da CPP, wadanda suka kebe wuraren nune-nune masu fadi a ciki, akwai wasu kamfanoni masu zaman kansu kamar su kamfanin fassara na StarTimes, da kamfanin Lishi na Beijing da sauransu, su ma sun samar da hotuna masu jawo hankalin 'yan kallo.

Dangote Sinatruk, kamfanin kera babbar mota ne da aka kafa ta hanyar zuba jari cikin hadin gwiwa tsakanin kasar Sin da Najeriya, yanzu haka yana samar da babbar mota mai amfani a kasuwanci a Lagos cibiyar tattalin arzikin Najeriya. Ko wace shekara adadin motocin da ya samar ya kai dubu 10. Manaja mai kula da aikin sayayya na kamfanin Adeola Adeokun ya gaya mana cewa, "Shawarar ziri daya da hanya daya tana da babbar ma'ana, yanzu muna gudanar da hadin gwiwa lami lafiya, har ma aikinmu ya samu kyautatuwa daga duk fannoni. Kamfanin da aka kafa bisa shawarar ya samar da guraben aikin yi da dama ga 'yan Najeriya, haka kuma ya kyautata rayuwarsu. Ana iya cewa, hadin gwiwar yana da makoma mai haske, kamfaninmu zai zama babban ci gaba a Najeriya, har ma da yammacin Afirka."

Yayin bikin nune-nunen, an kuma shirya taron dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar tattalin arziki da cinikayya dake tsakanin Sin da Najeriya a ranar 16 ga wata, inda mahalarta taron sun bayyana cewa, hadin gwiwar ya taka rawar gani ga sassan biyu a fannonin ci gaban tattalin arziki, da gina kayayyakin more rayuwa da zuba jari, da samar da aikin yi a Najeriya. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China