Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manama labaru da aka shirya a yau Laraba.
Kwanan baya ne, aka kafa majalisar soji ta wucin gadin kasar Sudan, tare da mika mulki cikin shekaru 2, inda suka yi alkawarin cewa, za a kafa gwamnatin fararen hula da za ta samu amincewar bangarori daban daban, wadda za ta mika mulki bayan kammala wa'adinta na mika mulki. (Bilkisu)