Lu ya bayyana haka ne a yayin taron manema labaru da aka shirya a yau Laraba.
Bayanai na cewa, gwamnatin Japan ta shirya aika kwararru a fannin kudi zuwa kasashen Afirka da suka karbi bashi daga kasar Sin, don taimaka musu warware matsalar kudin da suke fuskanta, kuma tana shirin gabatar da hakan a yayin taron kasa da kasa kan batun ci gaban Afirka da za a yi a birnin Tokyo a watan Agustan bana. Game da haka, Lu ya ce, yanzu kasashen Afirka na kokarin gaggauta bunkasa tattalin arziki da al'ummansu, kuma matsalar rashin kudi matsala ce da suke fuskanta. A matsayinta na abokiyar kasasen Afirka, kasar Sin na fatan karfafa hadin kai da kasashen Afirka a fannonin zuba jari da harkokin kudi, da kokarin taimakawa kasashen Afirka kan yadda za su kyautata muhimman kayayyakin more rayuwa da yanayin ci gaban tattalin arziki da na al'umma, don kara karfinsu da neman ci gaba. (Bilkisu)