A yayin ganawar, Wang ya bayyana cewa, shekara guda bayan farfado da huldar diplomasiyya a tsakanin Sin da Burkina Faso, kasashen biyu sun samu muhimmiyar nasara a fannin hadin gwiwa da juna. A cewar Wang, kasarsa tana goyon bayan matakan da Burkina Faso take dauka wajen neman ci gaba dake dacewa da halin da take ciki, da kokarin da gwamnatin kasar ke yi wajen kiyaye tsaro, bunkasa tattalin arziki da kuma kyautata zaman rayuwar jama'a.
Kasar Sin tana kuma fatan karfafa hadin kai dare da Burkina Faso bisa tsarin shawarar "Ziri daya da hanya daya", da tsarin dandalin tattaunawar hadin kai a tsakanin Sin da kasashen Afrika.
A nasa bangaren Barry ya bayyana cewa, kudurin da kasarsa ta yanke na farfado da huldar diplomasiyya tare da kasar Sin ya yi daidai. Kasar Burkina Faso na son karfafa hadin kai tare da Sin bisa tsarin shawarar "Ziri daya da hanya daya". (Bilkisu)