in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jimmy Carter Ya Zargi Kalaman Da Wasu 'Yan Siyasar Amurka Suka Yi Kan Kasar Sin
2019-04-17 17:18:56 cri

Jimmy Carter, tsohon shugaban kasar Amurka, ya bayyana a ranar Litinin da ta gabata cewa, shugaban kasar na yanzu Donald Trump, ya buga masa waya a karon farko a kwanakin baya, inda suka tattauna maganar kasar Sin. Yayin hirarsu Mista Trump ya bayyana damuwarsa kan yiwuwar kasar Sin ta zarce kasar Amurka. Sa'an nan Mista Carter ya ce ba ya damuwa kan yiwuwar ganin wannan batu ya abku. Ya ce "kasar Amurka ta riga ta zama kasa mafi son tayar da yaki a tarihin dan Adam", yayin da kasar Sin ba ta taba bata kudinta kan yaki ba, "wannan shi ne dalilin da ya sa suna gaba kuma muna baya." in ji Mista Jimmy Carter.

Lokacin da sakataren harkokin wajen kasar Amurka Mike Pompeo da sauran 'yan siyasa na kasar ke shafa wa kasar Sin kashin kaji a duk duniya, wannan furucin Mr. Carter, tsohon shugaban Amurka wanda ya taba kulla huldar diplomasiyya tsakanin Sin da Amurka a cikin wa'adin aikinsa, ya nuna hangen nesa da wani kwararre dan siyasa ke da shi, da kuma babban nauyin da ya sauke a wuyansa kan babbar moriyar Amurka. Da jin wannan maganar tasa, ya kamata wadancan 'yan siyasar Amurka marasa kula da muradun kasarsu su ji kunya sosai. Haka kuma lamarin da ya shaida cewa, tsoffin shugabannin Amurka da ma sauran masu sanin ya kamata, suna taka muhimmiyar rawarsu a kan batun daidaita dangantakar da ke tsakanin Sin da Amurka.

Karon farko ne Trump ya buga waya ga Jimmy Carter, tsohon shugaban kasar Amurka, inda ya bayyana masa damuwarsa, kana suka tattauna kan manufofi masu dacewa da ya kamata gwamnatin Amurka ta tsara kan kasar Sin.

Muna iya fahimtar irin damuwar da Trump ke da ita, wato, hakikanin gaskiya, Amurka ta dade tana zama kasa mafi karfi a duk fadin duniya, abun da ya sa ba ta saba da gogayya da wata kasa ba. A halin yanzu, jimillar tattalin arzikin kasar Sin ta riga ta zarce Yuan triliyan 90, wadda ta kai matsayi na biyu a duniya, al'amarin da ya kara janyo damuwar Amurka. Don haka wasu masu nuna tsattsauran ra'ayi a kasar Amurka sun yi amfani da wannan dama don kara taka rawarsu a fagen siyasa, kana, abun da suka yi, ya sa Amurka ta canja alkawarin da ta yi shekaru 40 da suka gabata lokacin da ta kulla huldar jakadanci da kasar Sin, wato ba ta dauki nauyin da ya kamata ta dauka a matsayin wata babbar kasa mai karfi a duniya ba, har ma ta ayyana kasar Sin a matsayin abokiyar takararta, da kaddamar da yakin cinikayya da shafa wa kasar Sin kashin kaji.

Amma, daga sauyin alakar dake tsakanin kasar Sin da Amurka a cikin shekara daya da ta gabata, an lura cewa, matakin matsa lambar da Amurka ta dauka bai haifar da sakamakon da take so ko kadan ba, a maimakon haka, tsohon shugaban Amurka Jimmy Carter ya taba yin kashedi sau tarin yawa cewa, kasar Sin tana taka rawar gani ga wadatar Amurka, inda ya ce, "Idan ba mu iya daidaita huldar dake tsakaninmu da kasar Sin yadda ya kamata ba, lamarin zai lalata kasashen nan biyu wato Sin da Amurka, musamman ma ga tattalin arzikin Amurka."

A cikin sabon rahoton hasashen tattalin arzikin duniya da asusun IMF ya fitar a makon jiya, an saukaka kason karuwar tattalin arzikin Amurka na bana zuwa kaso 2.3 bisa dari daga kaso 2.1 bisa dari, haka kuma an daga kason karuwar tattalin arzikin kasar Sin zuwa kaso 6.3 bisa dari daga kaso 6.2 bisa dari, har kasar Sin ta kasance kasa daya kacal wadda asusun IMF ya daga kason karuwar tattalin arzikinta a fadin duniya. Sakamakon nan ya sa gwamnatin Amurka ta damu matuka, har ta kara fahimta cewa, matsa lamba ga kasar Sin zai lalata moriyar kanta.

Sai dai yaya za a maida kasar Amurka ta sake zama matsayin koli a duniya? Mr Carter ya bada shawara cewa, bai kamata kasar Amurka ta kashe kudi da dama kan yake-yake ba, kada kuma ta tilastawa saura su bi ra'ayoyinta. Ya ce, idan aka yi amfani da kudin aikin soja dala triliyan 3 wajen raya ayyukan more rayuwar al'ummar kasar Amurka, mai yiwuwa ne za a kashe triliyan 2 kawai a wannan fanni. Amma za a samu hanyoyin motoci mafi sauri, da gadoji masu inganci, kana za a tabbatar da gyara hanyoyin motoci yadda ya kamata, da kuma raya tsarin bada ilmi na kasar mai kyau kamar kasar Koriya ta Kudu ko yankin Hongkong na kasar Sin.

Ko shakka babu, yi watsi da ra'ayin neman mallake duniya, ra'ayin kasancewar bangare daya, da kuma ra'ayin siyarar nuna karfin tuwo, tare kuma da dora muhimmanci kan moriyar jama'a, da kara karfin kanta na yin takarar, wannan ne hanyar da ta dace, wadda ta kamata Amurka ta dauka wajen kara neman ci gaba. A nata bangaren, kasar Sin na neman ci gaba ne da nufin biyan bukatun jama'arta na kyautata zaman rayuwa, amma ba kawo kalubale ko maimakon wani ba. Saboda muhimmin abun dake cikin al'adun gargajiyar kasar Sin shi ne, "Dora muhimmanci kan zaman lafiya", kasar Sin ba ta taba kai hari kan saura ba, tana fatan yin shawarwari kan manyan manufofin hadin kai, da kafa dandalin hadin kai, da kuma more nasarorin da aka cimma kan hadin kai tare da kasashe daban daban, kana da kafa makoma mai kyau irin ta bai daya ta bil adama, da kuma daukar nauyin dake bisa wata babbar kasa tare da Amurka.

Hakika, takarar dake tsakanin Sin da Amurka ba wani abu na ban mamaki ba ne, sai dai ya kamata ta kasance takara mai ma'ana, wato takara ce ta ci gaban kai, a maimakon takara ta nuna fin karfi. An lura da cewa, a yayin da shugaba Trump ya yi bayani a game da aikin bunkasa fasahar sadarwa ta 5G a kwanakin baya, ya ce, fasahar 5G wata gasa ce da dole ne Amurka din ta ci nasararta. Amma a watanni biyu da suka wuce, ya yi kira ga kamfanonin kasar Amurka da su ci nasarar fasahar ta hanyar yin takara a maimakon ta wasu hanyoyi da ba su dace ba. Idan hakan da gaske ne, to lalle takarar ta kasance yadda ya kamata ke nan.

A matsayinsa na shugaba na 39 na kasar Amurka, Mr. Jimmy Carter ya tuna da cewa, aiki mafi ma'ana da ya kammala a lokacin wa'adin mulkinsa shi ne "farfado da huldar da ke tsakanin Amurka da kasar Sin". To, kasancewarsa shugaba na 45 a tarihin kasar ta Amurka, ko akwai wani aiki mai ma'ana da Mr. Trump zai iya bayyanawa a lokacin da ya waiwayi baya a wata rana nan gaba?

(Masu Fassarawa: Kande, Lubabatu, Bello, Bilkisu, Murtala, Jamila, Zainab, ma'aikatan sashen Hausa na CRI)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China