in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Guterres ya yi kira a kara zuba jari domin samun ci gaba mai dorewa
2019-04-16 09:42:19 cri

A jiya Litinin ne babban sakataren MDD Antonio Guterres, ya bayyana cewa, ana bukatar karin jarin da za a zuba domin cimma maradun samun ci gaba mai dorewa na majalisar nan da shekarar 2030.

Guterres ya gabatar da wani jawabi, yayin bikin kaddamar da dandalin tattara jari domin samun ci gaba na shekarar 2019, wanda hukumar kula da tattalin arziki da zaman takewar al'umma ta MDD ta shirya jiya, inda ya bayyana cewa, bisa sakamakon sabon binciken da asusun ba da lamuni na duniya wato IMF ya fitar, an lura cewa, ko wace shekara kasashe masu tasowa suna fama da karancin kudin da yawansa ya kai dalar Amurka biliyan 2600 a bangarorin kiwon lafiya, da ba da ilmi, da ginin hanyoyi, da samar da wutar lantarki, da ruwa, da kayayyakin tsabtace muhalli.

Guterres ya kara da cewa, dole ne kasashe masu ci gaba su cika alkawarin da suka dauka a cikin ajandar aikin Addis ababa, domin samar da taimako na wajibi ga kasashe masu tasowa, musamman ma ga kasashen dake fama da tsananin talauci.

Babban jami'in ya ci gaba da cewa, idan kasashen duniya suka cimma nasara wajen dakile laifuffukan kaucewa biyan haraji, da halasta kudin haram da ake samu ba bisa ka'ida ba, da biyan kudi ba bisa ka'ida ba, irin kudin da za a samu daga hakan zai samar wa kasashe masu saurin ci gaban tattalin arziki wajababbun kudin hidimar jama'a, yayin da suke kokarin cimma burin samun dauwamammen ci gaba. (Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China