in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta ba da taimako wajen gina gada mai madaurai da ta fi girma a Afirka
2019-04-15 15:22:58 cri

Kasar Mozambique da ke kudancin nahiyar Afirka kasa ce da ta himmatu wajen sa hannu cikin aikin raya kasa bisa shawarar "ziri daya da hanya daya", kuma muhimmiyar kasa ce da ta hada kai da Sin wajen raya masana'antu. A 'yan shekarun da suka gabata, Sin da Mozambique suna ta inganta hadin kansu a fannonin aikin gona, makamashi da ma muhimman ababen more rayuwa. A ciki, gadar Maputo ta zama aiki mafi girma na raya ababen more rayuwa wadda kasar Sin ta taimaka wajen ginawa. Gadar ta fara aiki ne a watan Nuwamban shekarar 2018, lamarin da ya saukaka zirga-zirgar gabobi biyu na mashigin ruwan Maputo. Gadar kuma ta zama muhimmin bangare wajen hada arewaci da kudancin kasar, da ma kasar Afirka ta Kudu, wadda ke takawa muhimmiyar rawa wajen raya tattalin arziki da zamantakewar al'ummar Mozambique.

A kan mashigin ruwan Maputo da ke kudancin birnin Maputo, hedkwatar mulkin kasar Mozambique, ana iya ganin wata babbar gadar da ke hada da gabobin biyu. Ita ce gadar Maputo da kamfanin CRBC na kasar Sin ya taimaka wajen ginawa, kuma yanzu ta riga ta zama sabuwar alamar birnin. Gadar na da tsawon kilomita fiye da uku, wadda ta hada da cibiyar birnin Maputo da yankin Katembe da ke kudancin kasar. Kafin a gina gadar, jirgin fito ne kawai ake amfani da shi wajen sufuri, wanda ba ya iya daukan mutane da yawa, kuma ya kan kwashe dogon lokaci. Bayan gadar ta fara aiki kuwa, mintoci fiye da goma kawai ake kwashewa wajen zuwa wancan gefe, lamarin da ya saukaka zirga-zirgar gabobin biyu na mashigin ruwan Maputo. Rahotanni na cewa, yanzu akwai motoci fiye da 4000 da ke kai da dawowa a kan gadar.

Odorico Ernesto wani direban motar dakon kaya ya furta cewa, kafin a gina gadar, ya kan tuka mota har na tsawon awoyi shida daga Moamba zuwa Katembe, amma yanzu awoyi hudu ya isa, lamarin da ya sa ya ke iya kai da dawowa har sau biyu a yini guda, yawan kudin shiga da yake samu ya karu, zaman rayuwar iyalansa kuma ya kyautata. Ya ce,

"Bayan babbar gadar ta fara aiki, tsawon lokacin tuki ya ragu daga Moamba zuwa Katembe, kuma babu bukatar zabar wata hanya da ta fi nisa, an saukaka aikina sosai. Gadar Maputo na da matukar kyau, ina fatan kamfanonin Sin za su iya raya karin muhimman ababen more rayuwa a kasar Mozambique."

Wannan gadar mai madaurai da ta fi girma a Afirka, wadda ta kawo wa 'yan kasar Mozambique alheri na a zo a gani, an gina ta ne bisa ma'aunin fasahohin kasar Sin. Bai Pengyu, babban manajan ofishin kula da ayyukan Mozambique na kamfanin CRBC ya bayyana cewa, da farko dai bangaren Mozambique bai amince da ma'aunin fasahohin kasar Sin ba, amma Sin ta shaida masa ingancinsa bisa hakikanan abubuwa. Yana mai cewa,

"Bayan mun kammala ka'idojin gina gada bisa ma'aunin fasahohin kasar Sin, mun sake tantance su bisa ma'aunin na kudancin Afirka da na Turai domin shaida yiwuwar amfani da ma'aunin fasahohin Sin da ma tsaronsa. Lallai wannan aiki na da wuya sosai, domin mun kashe kusan shekara guda. Ko da yaushe muna kokarin amfani da ma'aunin fasahohin Sin a ketare. A lokacin farko, bangaren Mozambique da bangare mai sanya ido kan aikin ba su fahimci ma'aunin Sin ba, kana ba su amince da shi ba, amma daga baya sun canja ra'ayinsu. Gaskiya dai mun samu amincewa ne bisa abubuwan da muka yi a maimakon abubuwan da muka fada kawai."

Kamfanin kula da ayyukan gini na kasar Jamus na GAUFF na daya daga cikin bangarori masu sanya ido kan ingancin aikin gina gadar Maputo da kamfanin CRBC ya dauka, wanda ya sa hannu cikin aikin ginin a dukkan fannoni tun daga farko har zuwa karshe. Liu Nan daga kamfanin GAUFF ya gudanar da aikin sanya ido sau da yawa, kuma yana ganin cewa, aikin gina gadar Maputo yana daya daga cikin ingantattun ayyukan gini mafi kyau da ya taba sa hannu a ciki. 

"Kamfaninmu yana sanya ido ga ingancin ayyukan gini da dama na Afirka. Ina ganin cewa, gadar Maputo na da inganci sosai, wadda aka gina ta bisa tsauraran ma'auni. Sakamakon yanayin kasa da ma teku na wurin, an kago wasu sabbin fasahohi yayin da ake gina ta, wadanda ba a taba yin amfani da su ba, lamarin da ya sa aikin ya samu jinjinawa a duk duniya."

Ban da wannan kuma aikin gina gadar Maputo ya samar da dimbin guraben aikin yi ga mazauna wurin, an ce, yawan ma'aikata 'yan kasar da aka dauka sun zarce dubu uku. Felix Manhiga, wani ma'aikacin aikin da ya yi aiki har na tsawon shekaru hudu ya furta cewa,

"Kafin wannan aiki, ba ni da abin yi. Bayan shekaru hudu da na yi aiki a nan, na sayi fili, yanzu ina gina daki a kai. Yayin da nake aiki, na koyi wasu fasahohi, kamar na iya sarrafa wasu na'urorin inji. Ban da wannan, na koyi Sinanci, har ma na iya magana da shi."

Da haka ake da imanin cewa, gadar Maputo za ta taimaka wa kasar Mozambique wajen raya tattalin arzikinta, har ma ta samu ci gaba a dukkan fannoni.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China